<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>236</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) In san ka, Yesu, na ke so,
 Da ikon tashinka yanzu.
 In yi tarayya tare da kai
 A cikin naka raɗaɗi.

[V2]
 2) A iske ni a cikinka,
 Ba da adalcin kaina ba,
 Amma ta wurin bangaskiya
 Kullum in aikata nufinka.

[V3]
 3) Na duba ribar duniya,
 Ba za ta isa dogara ba,
 Dukan abu na lassafta
 Hasara domin saninka.

[V4]
 4) Na baya sai in manta fa,
 In kai ga ladan nasara.
 Ya Yesu, sai in nace bi
 Tare da kai, Ubangiji.</lyrics>
<title>In San Ka, Yesu, Na Ke So LW236</title>
</song>